Babban sifetan yan sandan Nigeria, Usman Alkali, ya sauyawa kwamishinan yan sanda na jihar Kano, Abubakar Lawal, wajen aiki zuwa jihar Ebonyi, sakamakon wani zargin rashawa da ake masa, wanda tuni babban sifetan ya bada umarnin gudanar da bincike.
Cikin wani Rahoto da jaridar Daily Nigerian ta rawaito, ya bayyana cewa, wata majiya ta tabbatar da cewa, babban sifeta ya tambayi wasu jami’ai na hukumar, inda suka tabbatar masa da abinda ake zargi.













































