Tinubu ya mika ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi

Abbas Sunusi 720x430

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana matukar alhininsa game da rasuwar Alhaji Abbas Sunusi, Galadiman Kano kuma babban dan majalisar sarki a masarautar Kano.

Sanusi, wanda ya rasu yana da shekaru 92 bayan doguwar jinya, ya rasu ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama, kamar yadda Mista Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana a ranar Laraba.

Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.

Shugaba Tinubu ya bayyana marigayi Sanusi a matsayin wani muhimmin ginshiki na cibiyar gargajiya, wadda za a rika tunawa da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gabanta fiye da masarautar Kano da ita kanta jihar.

Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Kano, Majalisar Masarautar Kano, da iyalan marigayin, inda ya yi addu’ar Allah ya ba wa marigayin Jannatul Firdaus.(NAN) (www.nannews.ng).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here