Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a sake bullo da shirin ciyar da daliban makaranta domin magance yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Idan dai za a iya tunawa gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari ta dakatar da shirin bayan shafe shekaru tana gudanar da shi.
Karanta wannan: Kotun ƙoli za ta sanar da ranar yanke hukuncin ƙarshe kan zaɓen gwamnan Kano
Amma Tinubu ya ba da umarnin maido da shirin, yana mai cewa zai taimaka wajen gyatta matsalar koyo da koyarwa.
Ya ce idan ba a magance matsalar koyo ba, zai yi wuya a magance kalubalen yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ne ya bayyana hakan a wani taron koli na ministoci kan abubuwan da za su aiwatar daga shekarar 2024 zuwa 2027.
Farfesa Mamman ya ce shugaban kasar ya ba da umarnin a cire shirin ciyar da dalibai daga ma’aikatar jin kai a mayar da shi ma’aikatar ilimi.