Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin alkalan kotun koli guda 11 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada domin cike gurbi a kujerar kotun koli.
Hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da aka karanta takardar da Tinubu ya aike zauren majalisar dattawan.
Tabbatar da hakan ya biyo bayan nazari da amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin shari’a, ‘yancin dan adam da kuma harkokin shari’a a yayi ranar Alhamis.
Tinubu ya bukaci majalisar dattijai da ta tabbatar da sunayen wadanda majalisar shari’a ta kasa ta ba su shawarar su cike mukaman da wasu alkalai suka mutu da murabus.
Wadanda aka tantance din sun hada da Mai shari’a Haruna Tsammani (Arewa maso Gabas), wanda ya jagoranci kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, Mai shari’a Moore Adumein (Kudu-Kudu), Mai Shari’a Jummai Sankey (Arewa ta Tsakiya), Mai Shari’a Chidiebere Uwa (Kudu maso Gabas); da Mai shari’a Chioma Nwosu-Iheme (Kudu maso Gabas)
Sauran sun hada da Justice Obande Ogbuinya (Kudu-maso-Gabas), Justice Stephen Adah (Arewa Ta Tsakiya), Mai Shari’a Habeeb Abiru (Kudu maso Yamma), Mai Shari’a Jamilu Tukur (Arewa maso Yamma), Mai Shari’a Abubakar Umar (Arewa-maso-Yamma) da Mai Shari’a Mohammed Idris (Arewa-Tsakiya) ).
Shugaban kwamitin, Sanata Tahir Monguno (APC, Borno), a lokacin da yake gabatar da rahoton kwamitin, ya ce wadanda aka nada suna da cancanta da gogewar da ake bukata don samun mukamin, kuma babu koke a kansu.













































