Cikin bidiyo: An fara gwaji a Matatar mai ta Fatakwal

Port Harcourt Refinery 750x430
Port Harcourt Refinery 750x430

Tsohon Shugaban kungiyar dillalan man fetur IPMAN a Jihar Ribas, Dakta Joseph Obele, ya ce an kammala aikin gyaran matatar mai ta Fatakwal kuma an fara gwaji.

Obele, wanda kungiyarsa ta samu cikas a lokacin da yake rike da mukamin Shugaban kungiyar IPMAN a jihar, ya ce a yanzu haka an fara gwajin kashin farko na aikin gyaran.

Wa’adin kammala aikin watan Disamba da gwamnatin tarayya ta kayyade ya zama wani batu na cece-kuce a yayin da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur ke bayyana kakkausar suka kan wa’adin.

Karanta wannan: Shugaba Tinubu ya sake gabatar da shirin ciyar da Yara makaranta

Karamin Ministan Mai, Sanata Heineken Lokpobiri, a ziyarar da ya kai matatar ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a kammala aikin gyaran kashin farko a watan Disambar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here