Yanzu-yanzu: Matashin da ake zargi da kashe sojoji 17 ya magantu

Fuskar, Dan Ta'adda, zargi, kashe, sojoji
Wanda ake zargin shugaban kungiyar 'yan ta'adda ne da suka kashe sojoji 17 kwanan nan a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta, ya...

Wanda ake zargin shugaban kungiyar ‘yan ta’adda ne da suka kashe sojoji 17 kwanan nan a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta, ya fito domin tabbatar da matakin da suka dauka.

A cikin wani faifan bidiyo na TikTok, matashin wanda bai damu da rufe fuskarsa ba, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa sojojin da aka kashe na aikin samar da zaman lafiya ga al’umma.

Karin labari: ‘Yan Sanda: Jaruma Amal ta gurfana a kotu kan zargin bawa ɗan sanda cin hanci

Ya yi ikirarin cewa sun je can ne domin su yi fada a madadin al’ummar Okoloba da ke makwabtaka da su a rikicin filaye da ya kaure. Yayin da Okuama ke Urhobo, Okoloba kuma Ijaw ne.

A cewar shugaban kungiyar, wanda ya ce mahaifinsa, Kyaftin din sojan Najeriya mai ritaya, ya rasu a shekarar da ta gabata, ya ce tun da farko sojoji sun zo sun kwashe wasu mutane suna zargin sun kashe su, amma sai suka dawo suka kama shugabannin al’ummar Okuama.

Karin labari: Kotu ta umarci NYSC ta bawa mata damar sanya riga da siket

Da yake magana da Turancin Pidgin, ya fada a cikin faifan bidiyon, wanda ya sha cewa zai zama na karshe.

Shugaban ‘yan kungiyar ya ce a halin da ake ciki, ba su yi nadamar kashe sojojin ba.

Mutanen 17 da aka kashe, dukkansu na Bataliya ta 181, an kashe su ne a ranar 14 ga watan Maris.

Karin labari: An bude shagon barasa na farko a Saudiyya

A cikin wata sanarwa mai taken “Ku huta lafiya, Jarumanmu da suka mutu”, rundunar sojin Najeriya ta bayyana wadanda harin ya rutsa da su a matsayin kwamandan bataliya ta 181.

Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da farautar wadanda ake zargin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here