Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega ya samu sabon mukami

Attahiru Jega
Attahiru Jega

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya amince da nadin Farfesa Attahiru Jega a matsayin Uban Jami’ar Jihar Nasarawa dake Keffi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Malam Aliyu Ubandoma, ya fitar ranar Alhamis a garin Lafiya.

Ubandoma ya ce gwamnan ya amince da nadin ne a wani mataki na ganin gwamnati ta samar da ingantaccen ilimi a jami’ar.

Karanta wannan: Cikin bidiyo: An fara gwaji a Matatar mai ta Fatakwal

Ya ce gwamnan ya kuma amince da nadin Shuaibu Kore, Mista Thomas Ogiri da da kuma Mary Enwongulu a matsayin mambobin majalisar gudanarwar jami’ar.

Ya ce za a sanar da ranar kaddamar da majalisar gudanarwar jami’aar a nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here