Tuna Baya: Yadda Shugaba Tinubu da tawagarsa ke zanga-zangar matsin rayuwa a 2012

Tuna Baya, yadda, Shugaba, Tinubu, tawagarsa, zanga-zangar, matsin, rayuwa
A kwanakin baya ne dai kafafen sada zumunta suka taru bayan samun labarin wata zanga-zanga da matasan Najeriya ke shirin yi a fadin kasar.   Zanga-zangar...

A kwanakin baya ne dai kafafen sada zumunta suka taru bayan samun labarin wata zanga-zanga da matasan Najeriya ke shirin yi a fadin kasar.

Zanga-zangar wacce aka bayyana a ranar 1 ga watan Agusta ita ce nuna rashin gamsuwarsu kan tsadar rayuwa da karancin abinci da rashin aikin yi da kuma rashin gudanar da mulki a kasar.

Da yake mayar da martani game da kiraye-kirayen da aka yi na zanga-zangar da aka shirya a shafin X, Bayo Onanuga, mashawarci na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan bayanai da dabaru, ya bayyana kiraye-kirayen zanga-zangar da aka yi a fadin kasar nan karkashin maudu’in #TinubuMustGo da #Revolution2024 a matsayin cin amanar kasa.

Karin labari: Jihohi 20 a Najeriya ciki harda Kano sun samu sabbin kwamandojin FRSC

Sai dai SolaceBase ta tuna cewa a shekarar 2012, Tinubu, wanda a wancan lokacin shi ne jagoran jam’iyyar ACN na kasa, tare da magoya bayansa sun jagoranci gangamin #OccupyNigeria don nuna adawa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na wancan lokacin saboda yanke shawarar cire tallafin mai.

Daga baya aka yada zanga-zangar neman kawar da tallafin domin tsige Jonathan da Jam’iyyarsa ta PDP.

Sannan Tinubu ya zargi gwamnatin Jonathan da cin amanar kwangilolin da ta kulla da jama’a ta hanyar cire tallafin man fetur kwatsam.

Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya ta yi barazanar daukar mataki kan wasu hukumomi da kamfanoni

Hasali ma, Onanuga daya nemi ‘yan Najeriya da kada su shiga zanga-zangar watan Agusta ya rubuta a shekarar 2012 cewa “Wanda ya shuka guguwa zai girbe guguwa. Don haka bari ya kasance ga Mista Goodluck Jonathan da majalisar ministocinsa.” Ya rubuta a shafin X ranar 3 ga watan Janairu, 2012 don nuna goyon baya ga zanga-zangar ƙasar baki ɗaya.

Shekaru goma sha biyu bayan haka,  Onanuga yana yin kaca-kaca da wata zanga-zangar adawa da gwamnatin da yake aiki a karkashinta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here