Takardar shaidar NBAIS daidai take da WAEC da NECO – Jami’i

NBAIS New 692x430 (1)

Wani jami’in hukumar kula da jarrabawar kammala sakandare bangaren harshen larabci da addinin musulunci ta kasa (NBAIS) ya ce takardar shaidar hukumar ba ta yi kasa a daraja da takardar shaidar kammala jarrabawar Afirka ta Yamma ba (WAEC) da kuma (NECO).

Mataimaki na musamman ga magatakardar hukumar, Ustaz Abdul-Lateef Adekilekun ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin a Osogbo.

Adekilekun ya ce duk da dadewa da hukumar ta yi da kuma karramawar da gwamnatin tarayya ta yi, yawancin manyan makarantun kasar nan ba sa karbar takardar shaidar domin baiwa dalibai damar shiga jami’a.

A cewarsa, manyan makarantun da ke fadin kasar nan na bukatar karin fadakarwa kan sahihanci da karbuwar takardar shaidar.

Karin karatu: Kwalejojin ilimi a Najeriya za su fara ba da shaidar digiri

An kafa hukumar da farko a matsayin Hukumar kula da Larabci da Ilimin Musulunci (BAIS) a shekarar 1960, musamman s Arewacin Najeriya.

“A shekarar 1967 aka mayar da hukumar zuwa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) sakamakon kirkiro jihohi.

“Amma a shekarar 2011, bayan shafe shekaru 40 da kafa hukumar a karkashin ABU, hukumar ta zama ta kasa ma’aikatar ilimi ta tarayya ta amince da ita a matsayin hukumar jarrabawa.

“Hukumar ta zama daidai da WAEC da NECO, mai hedikwata a Kaduna,” inji shi.

Mataimaki na musamman ya kara da cewa a shekarar 2017 hukumar ta zama mai cin gashin kanta kamar WAEC, NECO kuma an amince da takardar shaidar a duniya.

“Saboda umarnin Gwamnatin tarayya da Hukumar Jami’o’i ta Kasa (NUC) ya sa jami’o’i da dama a Arewa da wasu na Kudu ke karbar takardar shaidar NBAIS.

“Amma karbuwarsa ba kamar yadda ake tsammani ba duk da amincewar gwamnatin tarayya da NUC,” in ji shi.

Adekilekun, ya bayyana cewa hukumar ta shirya hada ilimin Larabci da ilimin kasashen yamma, ya ce jihohi 26 a Najeriya na rubuta jarabawar NBAIS tare da makarantu 1,200 masu alaka da su a fadin kasar.

“Ya kuma ce, Kiristoci da Musulmi da suke makarantar sun yi karatun Islamiyya da Larabci da duk wasu darussa na al’ada kamar lissafi, Turanci da sauransu.

Sai dai mataimaki na musamman ya roki Gwamnatin Tarayya da ta kafa kwamitin wayar da kan jama’a, wanda ya hada da wadanda aka yi wa jarrabawa da kuma amana da za su fara rangadin manyan makarantun kasar baki daya. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here