Kamfanin sukari na Dangote ya himmatu wajan kara habbaka shirye-shiryen sa na taimakon jama’a a tsakanin al’ummomin da ke zaune a jihohin Adamawa da Nasarawa.
Kamfanin ashirye shirye-shiryen sa na sanya hannun jari dan samar da danyen sukari a matsayin wani bangare na habbaka samarda sukari na Gwamnatin Tarayya.
Wannan na zuwa ne bayan sanya dala miliyan 500 da aka saka a cikin aikin da ake aiwatarwa a jihar Nasarawa
Kamfanin yace ya samar da wata taswirar tabbatar da dogaro da kai a fannin sikari cikin kankanin lokaci, wanda ya kai ga samar da tsarin sarrafa sukari a Najeriya.
Rahoton yace an kashe biliyoyin nairori a shirye-shiryen shiga tsakani da al’ummomin da ke karbar bakuncin shirin a Numan dake Adamawa, da aikin Tunga a jihar Nasarawa.
Kamfanin ya ce ya samar da kadada 78,000 na gonaki a Nasarawa da kuma hekta 32,000 a Adamawa akokarin samar da dubunnan ayyukan yi ga ‘yan Najeriya.
A halin yanzu akwai sama da ma’aikata 600 da ake daukar nauyin aikin su, yayin da ake shirin samar da wutar lantarki mai karfin Megawata 90 a aikin samarda sukarin Dangote da ke Tunga a Jihar Nasarawa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa rukunin kamfanin Dangote ne na biyu wajen daukar ma’aikata aiki bayan Gwamnatin Tarayya.
Da yake jawabi a taron shekara-shekara na kamfanin a kwanakin nan, shugaban matatar sukari na Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa Najeriya za ta iya samun canjin kudaden waje na dala miliyan 700 a duk shekara daga tsarin BIP.
Ya yi gargadin cewa dole ne a kare tsarin BIP don dakile tattalin arzikin Najeriya da samar da ayyukan yi.
Anasa bangaren Ministan Masana’antu, Ciniki, da Zuba Jari, Otunba Niyi Adebayo wanda ya kai ziyarar aiki a babban kamfanin Dangote na Savannah da ke Numan a Jihar Adamawa,da kuma cibiyar aikin sukari na Tunga a Jihar Nasarawa, ya bayyana irin ayyukan a matsayin “babba al’amari, mai ban sha’awa da ban mamaki.”













































