Shugaban hukumar kiyaye hadura ta Najeriya rashen jihar Cross River, Mista Maikano Hassan, ya tabbatar da faruwar hatsarin da ya yi sanadiyar rasuwar wata mata a Calaba ranar Lahadi.
Ya yin da yake magana da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, Hassan ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun da ya wuci kima da matar takeyi a motar ta.
Ya kara da cewa an garzaya da ita asibiti wanda nan take bayan kai ta asibitin ta mutu sakamakon munanan raunika da suke jikinta.
Kamfanin dillancin labarai ya tattaro bayanan cewa matar ta bi sahun mijinta ne wanda take zargin sa da karuwa a cikin motar sa, hakan yasa take bin motar da gudu domin ta rutsa su.
NAN













































