Jam’iyyar PDP zata gudanar da taron kwamitinta na zartarwa a ranar 4 ga Mayu

PDP PDP 1
PDP PDP 1

Jam’iyyar PDP za ta gudanar da babban taron kwamitin zartarwata na kasa karo na 96, a ranar Laraba 4 ga watan Mayun shekarar 2022.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakatarenta na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Anyuwa ya bukaci daukacin mambobin kwamitin da su halarci taron.

Ya ce za a fara gudanar daa taron ne da karfe 2 na ranar kuma zai gudana ne a dakin taro na Sakatariyar PDP ta kasa dake Wadata Plaza, a birnin tarayya Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya rawaito cewa duk da yake ba a fadi abubuwan da za a tattauna a wajen taron ba, amma dai ana tsammanin za a tattauna batutuwan da suka shafi Babban zaben shekarar 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here