Hukumar NDLEA ta kama Cocaine kilogiram 511 da tabar wiwi a Kaduna

1kg of cocaine seized by NDLEA operatives in Kaduna.
1kg of cocaine seized by NDLEA operatives in Kaduna.

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta kama kilogiram ɗaya na hodar iblis da kilogiram ɗari biyar da goma sha ɗaya da ɗigo uku na tabar wiwi a jihar Kaduna a ranakun Laraba da Alhamis, kamar yadda kwamandan hukumar, Malam Umar Adoro, ya shaida wa taron manema labarai yau Asabar.

Adoro ya ce, jami’an hukumar sun kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1 tare da kama wasu mutane biyu da ake zargi a tashar mota ta Mando da ke babban birnin jihar ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa a ranar 11 ga wannan wata da muke ciki na Afrilu jami’ansu sun cafke kilogiram 441 na tabar wiwi daga hannun wani da ake zargi.

A ranar Laraba, sun sake kama kilogiram 12.1 tare da cafke wani da ake zargi, Adoro ya ce, an kama mutanen biyu a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Haka kuma ya shaida wa manema labarai cewa, a ranar 17 ga watan Afrilu, jami’an NDLEA sun kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram uku lokacin da suka cafke wani mutum da ake zargi a hanyar Makarfi da ke unguwar Rigasa a babban birnin jihar ta Kaduna.

Haka zalika a ranar 21 ga Afrilu, jami’an hukumar sun kama kilo 10.6 na tabar wiwi tare da kama wani da ake zargi a ƙauyen Kargi da ke karamar hukumar Kubau ta jihar.

Kwana guda gabanin haka, an kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 44 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, kuma an kama wani da ake zargi a nan ma.

Adoro ya ce, an kama jimillar tabar wiwi mai nauyin kilogiram 511.3 a jihar Kaduna tsakanin ranar 11 ga wannan wata da muke ciki na Afrilu zuwa Juma’a 22 ga wata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here