Shahararriyar mawakiyar Musulunci ta Najeriya, Rukayat Gawat Oyefeso ta rasu.
Rukayat ta shahara da murya mai kayatarwa wajan wakar addin musulunci.
An sanar da cewa ta rasu ne a safiyar ranar Talata.
Babban mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas, Jubril Gawat, wanda dan uwan marigayiyar ne ya tabbatar da rasuwar ta.