PDP ta zabi Kale Kawu a matsayin dan takarar gwamna na masalaha a zaben 2027

1779550349780 750x430

Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ta zabi Injiniya Kale Kawu a matsayin dan takarar gwamna na yar masalaja na babban zaben shekarar 2027.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma jagoran jam’iyyar a jihar, Dakta Bukola Saraki, ne ya sanar da zabin a wata sanarwa ranar Asabar.

SolaceBase ta ruwaito cewa sanarwar da Saraki da kansa ya sanya wa hannu ta cewa: “Ina farin cikin sanar da cewa, bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsakin jam’iyyar PDP a Kwara da manyan ‘yan takarar mu na gwamna, mun cimma yarjejeniya kan wanda zai dauki tutar jam’iyyarmu mai girma a zaben gwamna mai zuwa.

Wancan dan takarar shi ne Injiniya Kale Kawu.

“Ina mika godiya ta ga sauran ‘yan takara wadanda, saboda maslahar jam’iyyarmu da jihar mu, suka yi janye cikin mutunci domin tallafa wa wannan yarjejeniya. Wannan ruhin hadin kai da sadaukarwa ne zai kai mu ga nasara.”“Ina yi wa dukkan mambobin mu, wakilai, da magoya baya fatan gudanar da zaben fidda gwani na gwamna da za ayi gobe cikin nasara, lumana, da tsari.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here