Gwamna Namadi ya amince da nadin sabon Sarkin Gumel

Gumel 507x430

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Gumel na 17, kwanaki 3 bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi Sarkin Gumel.

Sakatariyar Gwamnatin Jihar, Bala Ibrahim ne ya sanar da nadin a ranar Lahadi yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatarewar Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa (NUJ) da ke Dutse.

Ibrahim ya ce an yi nadin ne bayan tuntubar Majalisar Masarautar Gumel da masu zaben sarki, kuma bisa ga Dokar Majalisar Masarautu ta Jihar Jigawa.

“Bayan gudanar da cikakkiyar tuntuba da Majalisar Masarautar Gumel da masu zaben sarki, bisa ga Dokar Majalisar Masarautu ta Jihar Jigawa, Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin sabon Sarkin Gumel,” in ji shi.

Sakataren ya ce nadin zai fara aiki nan take domin cike gibin jagorancin da rasuwar tsohon Sarkin ta haifar, da kuma tabbatar da ci gaba, zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautar.

Ya bayyana sabon Sarkin a matsayin wanda ya cancanta, inda ya bayyana cewa ya taba zama Ciroman Gumel a zamanin mulkin marigayi mahaifinsa.

A cewarsa, kwarewar Dr. Lawan, iliminsa da sanin al’adu da tarihin Gumel ne suka sa ya cancanci wannan mukami.

“Da yake ya taba zama Ciroman Gumel, Dr. Lawan ba sabo ba ne ga jama’a. Ya san kalubale da burin mutanen Gumel da na Jihar Jigawa baki daya. Gwamnati na da yakinin cewa zai yi jagoranci mai ma’ana da kwazo,” in ji Ibrahim.

Ya ce gwamnati na sa ran sabon Sarkin zai kara karfafa abin da ya gada daga wanda ya gabata, sannan ya ba da gudummawa wajen zaman lafiya da ci gaban masarautar.

Sakataren ya ce Gwamna Namadi ya yi kira ga al’ummar Masarautar Gumel da su ba sabon Sarkin cikakken goyon baya da hadin kai.

“Mai Girma Gwamna na kira ga al’umma maza da mata na Masarautar Gumel da su ba sabon Sarkin cikakken goyon baya da hadin kai domin samun zaman lafiya da ci gaban masarautar,” in ji shi.

Ibrahim ya kuma yi addu’a ga marigayi Sarkin, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen karfafa tsarin gargajiya a matsayin masu kiyaye al’adu da hadin kai.

Ya ce Gwamna Namadi zai mika sandar mulki ga sabon Sarkin a wani biki da ya dace da matsayinsa a cikin lokaci.

Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a masarautar da su ba gwamnati hadin kai domin tabbatar da gudanar da bikin nadin sarauta cikin lumana da nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here