Shettima ya bar Abuja domin wakiltar Tinubu a taron G20 a Afirka ta Kudu

Shettima departs new 750x430

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bar Abuja domin wakiltar shugaban kasa Bola Tinubu a taron shugabannin ƙasashe na G20 da ake shirin gudanarwa daga ranar Asabar 22 zuwa Lahadi 23 ga watan Nuwamba a birnin Johannesburg na ƙasar Afirka ta Kudu.

A cewar Stanley Nkwocha mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, ofishin mataimakin shugaban kasa ya tabbatar da cewa wannan tafiya ta Shettima ta biyo bayan matsayar shugaban kasa Tinubu na ci gaba da kasancewa a Najeriya saboda kula da batutuwan tsaro da suka taso a ƙasar.

Nkwocha ya bayyana cewa shugaban kasa Tinubu ya ɗage tafiyarsa zuwa Johannesburg domin jiran ƙarin bayanan tsaro game da lamuran tsaro da suka faru kwanan nan a jihohin Kebbi da Kwara, waɗanda suka jawo damuwa a tsakanin jama’a da hukumomi.

Labari mai alaƙa; Rashin tsaro: Tinubu ya dage tafiyarsa zuwa taron G20 da AU-EU

Ya ce shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ke rike da jagorancin ƙungiyar G20 a wannan shekarar, shi ne ya aikawa shugaban kasa Tinubu gayyata domin halartar taron, wanda ke haɗa manyan shugabanni daga manyan kasashe masu tattalin arzikin duniya 20, haɗe da ƙungiyoyin Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka da kuma cibiyoyin kuɗi na duniya.

Taron zai baiwa kasashe damar tattaunawa kan manufofi da matsalolin tattalin arziki da tsaro da suka shafi sassan duniya, tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe masu tasiri.

Mataimakin shugaban kasa Shettima zai dawo Najeriya bayan kammala zaman tarurrukan da aka shirya a birnin Johannesburg.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here