Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai, ta zargi makarantar da rashin bin umarnin tsaro 

Bago 750x430

Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace adadin ɗalibai da malamai da ba a tabbatar da yawansu ba daga makarantar St. Mary’s da ke unguwar Papiri a karamar hukumar Agwara.

Wannan lamari gwamnati ta bayyana shi a matsayin abin takaici kuma wanda za a iya kaucewa.

Gwamnatin ta ce har yanzu ana jiran cikakken bayanin yawan mutanen da aka sace yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da tantancewa.

Sanarwar da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abubakar Usman ya fitar ta nuna cewa harin ya faru duk da bayanan sirri da suka nuna karuwar barazana a yankunan dake mazabar Neja ta Arewa.

Gwamnatin ta ce tun farko ta bayar da umarnin tsaro da ya haɗa da dakatar da duk ayyukan gine-gine da rufe dukkan makarantun kwana a yankin.

Gwamnatin ta bayyana cewa duk da wannan umarni, makarantar St. Mary’s ta koma gudanar da karatu ba tare da sanarwa ko neman izini daga gwamnati ba, lamarin da ya sanya ɗalibai da malamai cikin haɗari.

Gwamnatin ta ce hukumomin tsaro sun kaddamar da bincike kai tsaye da aikin ceto domin tabbatar da kubutar da duk waɗanda aka sace.

Ta ƙara da cewa tana ci gaba da mu’amala da hukumomin tsaro, tare da alkawarin sanar da jama’a duk wani sabon bayani da zai fito.

Hukumomi sun yi kira ga masu makarantu, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su bi umarnin tsaro yadda ya kamata, domin kare rayukan jama’a musamman yara.

Rahotannin cikin gari sun nuna cewa harin ya faru tsakanin ƙarfe biyu zuwa uku na dare ranar Juma’a, inda aka ce da yawa daga cikin ɗalibai ne.

Har yanzu ba a samu rahoton adadin waɗanda aka sace ba saboda ana tattara bayanai.

Shugaban sashen kula da bala’i da tallafi na karamar hukumar Agwara, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, inda ya ce har yanzu ana tantance adadin ɗalibai da malamai da aka sace.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Wasiu Abiodun ya ce za a fitar da bayanai daga baya, yayin da wannan lamari ke zuwa kwanaki kaɗan bayan sace ɗalibai 25 a Maga, jihar Kebbi, wanda ya ƙara tayar da hankalin jama’a game da matsalolin tsaro a makarantun arewacin ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here