Majalisar dattijai zata tan-tan-ce sababbin ministocin da Buhari ya aike mata da sunayen su sati mai zuwa

Ahmed Lawan
Ahmed Lawan

Shugaban majalisar dattijai, Ahanad Lawan,  ya ce majalisar zata tantanci wadan da Buhari ya tura mata sunayen su a matsayin wadan da zai nada su mukamin ministoci, a ranar 29 ga watan June.

Shugaban majalisar ya sanar da hakane kafin majalisar ta dage zamanta zuwa June 28 na shekarar 2022.

A wata wasika mai dauke da kwanan wata 15 ga watan June 2022, da shugaban kasa Buhari ya aikewa majalisar, ya bukaci majalisar da ta tabbatar da na din nasu.

Wa danda majalisar zata tantanci sune, Henry Ikechukwu Ikoh (Abia), Umana Okon Umana – (Akwa Ibom)  Ekumankama Joseph Nkama- (Ebonyi) da kuma Goodluck Nanah Opiah (Imo)

Sauran sun hada da Umar Ibrahim El-Yakub (Kano) Ademola Adewole Adegoroye  (Ondo) da kuma Odum Udi ( Rivers).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here