APC Plateau: Kwamiti ya karyata sakamakon da aka fitar a baya, ya ayyana Gagdi a matsayin wanda ya yi nasara

Hon Yusuf Gagdi 750x430

Shugabar Kwamitin Zaben Fidda Gwanin Jam’iyyar APC na Jihar Plateau, Stella Okotete, ta karyata sakamakon da aka fitar a baya na zaben fidda gwanin ‘Yan Majalisar Wakilai na kananan hukumomin Pankshin/Kanke/Kanam (PKK), inda ta bayyana shi a matsayin na bogi.

Kwamitin ya kuma ayyana Hon Yusuf Gagdi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben fidda gwanin.

Okotete, wacce ta yi jawabi ga manema labarai a Jos a ranar Litinin, ta bayyana cewa Nandom Andrew Kura, wanda aka nada a matsayin jami’in da ke da ikon bayyana sakamakon a hukumance ne kawai ke da ikon ayyana sakamakon zaben fidda gwanin bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Ta jaddada cewa duk wata sanarwa da aka yi a baya wanda ba daga nan ta fito ba, ba ta da inganci kuma ayi watsi da ita.

Biyo bayan wannan bayani, Kura, wanda shi ne babban jami’in da ke da alhakin bayyana sakamakon a hukumance, ya ayyana Yusuf Gagdi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben fidda gwanin APC na kananan hukumomin PKK da aka gudanar a ranar Asabar.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ayyana sakamakon, Gagdi ya ce an gudanar da zaben yadda ya kamata a dukkan mazabu 36, tare da samun hujjoji ciki har da bayanan tantancewa, bidiyo, da hotuna domin tabbatar da sahihancin zaben.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here