Dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyya NDC, Senata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyar girmamawa ga tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a daren Alhamis bayan ya sauka a Kano.
Mai taimakawa Kwankwaso a bangaren yada labarai, Saifullahi Hassan ne ya bayyana ziyar a cikin sanarwa, inda ya ce tsohon gwamnan Kano ya gana da Obasanjo ne a gidansa, inda tsohon shugaban kasar yake zama idan ya ziyara zuwa jihar.
Sanarwar ta ce haduwar ta ba da damar tattaunawa da musayar ra’ayi cikin zumunci tsakanin shugabannin biyu.

SolaceBase ta rawaito cewa Kwankwaso da Obasanjo suna da alaka a siyasance da ta dade sama da shekaru goma.
A zamanin mulkin Obasanjo, Kwankwaso ya yi aiki a matsayin Ministan Tsaro tsakanin 2003 zuwa 2007 bayan ya kammala wa’adinsa na farko a matsayin gwamnan Jihar Kano.
‘Yan siyasar biyu sun ci gaba da mutunta juna tsawon shekaru duk da cewa sun kasance a jam’iyyu daban-daban a lokuta daban-daban.
A cewar sanarwar, Obasanjo ya kawo ziyara jihar Kano ne domin wani aiki na hukuma a yanzu haka.
Sanarwar ta ce a yayin ziyarar, Kwankwaso na tare da Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo, dan takarar NDC na kujerar Gwamnan Jihar Kano.
“A daren nan Mai Girma Sen. Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, dan takar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar NDC, ya kai ziyar girmamawa ga jigo kuma tsohon Shugaban Najeriya, Mai Girma Olusegun Obasanjo, GCFR, a gidansa na Kano,” in ji sanarwar.
Ba a bayyana cikakken bayani kan abin da suka tattauna ba kawo yanzu.
















































