Jam’iyyar PDP a Kaduna ta dakatar da sakatarenta saboda zargin yi mata adawa

PDP PDP 750x430

Jam’iyyar (PDP) a jihar Kaduna ta dakatar da sakatarenta na jiha, Malam Sa’idu Adamu, bisa zargin yin adawa da jam’iyya da kuma aikata manyan laifuka na rashin ɗa’a.

Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Hajiya Maria Dogo, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Kaduna a ranar Talata.

Ta ce an dauki wannan mataki ne bisa tanade-tanaden Sashe na 58(1)(h) da Sashe na 57(3) na tsarin mulkin jam’iyyar PDP na shekarar 2017 (wanda aka gyara).

Dogo ta bayyana cewa kwamitin aiki na jiha (SWC) ne ya yanke wannan hukunci a zaman da aka gudanar ranar Litinin, 6 ga Oktoba, 2025, a sakatariyar jam’iyyar da ke Kaduna.

Ta ce dakatarwar za ta fara aiki nan take, kuma za ta ɗauki tsawon wata guda yayin da ake gudanar da bincike kafin a yanke hukunci na ƙarshe daga jam’iyyar.

Ta kara da cewa a wannan lokaci, an haramta wa Sa’idu Adamu halartar ko wane taron jam’iyya a kowane mataki.

Jam’iyyar ta tabbatar wa mambobinta da jama’a cewa tana ci gaba da tabbatar da ɗa’a, gaskiya da adalci a cikin ayyukanta a ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar na jiha, Mista Edward Percy Masha.

Ta kuma ce ƙoƙarin da kwamitin aiki na jiha ke yi yanzu na nufin ƙarfafa jam’iyyar da tabbatar da gaskiya da riƙon amana tsakanin dukkan matakan shugabanci.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here