A ranar Litinin ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC ta gurfanar da Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, Rochas Okorocha a gaban kotu.
Hukumar tana tuhumar tsohon gwamnan jihar Imo ne da laifuka 17 a wata babbar kotun tarayya dake Abuja.
EFCC ta ce tsohon gwamnan na Imo ya hada baki da jam’iyyar APC da wasu kamfanoni guda biyar, domin sace naira biliyan 2.9 na al’umma.
Baya ga Okorocha, sauran wadanda ake tuhuma sun hada da Anyim Nyerere Chinenye, Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited, da Legend World Concepts Limited.
A watan Afrilun 2021, EFCC ta kama tsohon gwamnan kuma an gurfanar da shi na tsawon kwanaki biyu bisa wasu batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa.
Solacebase ta ruwaito cewa Okorocha, wani jigo a jam’iyyar APC kwanan nan ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.













































