Ku Buga kididdigar asusun jami’ar- ASUU ta kalubalanci hukumar jami’ar Kano

ADC9978C D280 4E68 B854 839EF179389A
ADC9978C D280 4E68 B854 839EF179389A

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano, Wudil, ta kalubalanci hukumomin jami’ar da su bayyana wa jama’a, kididdigar asusun jami’ar na shekaru 7 da suka wuce.

Kungiyar ta ce jami’ar na samun kudade ne daga rijistar dalibai, wanda akasari aka karkatar da su kamar yadda rahoton kwamitin sa ido da aiwatar da kasafin kudi na jami’ar na 7 da 8 ya nuna.

Kungiyar ASUU reshen Wudil a wata sanarwa da shugaban kungiyar Muhammad Sani Gaya da Murtala Muhammad suka fitar a ranar Lahadin da ta gabata sun mayar da martani dangane da wata sanarwa da mahukuntan jami’ar suka fitar na cewa ta kungiyar ta mayar da hankali kan abin da ya shafe ta tare da tsayawa kan gaskiya da rikon amana ba wai yin rikom sakainar kashi wajen tafiyar da harkokin jami’ar ba.

A cewar ASUU Hukumar jami’ar ta batar da kudade masu yawa ta hanyar da bata dace ba, wanda hakan ya jefa jami’ar a wani hali.

Sanarwar ta kara da cewa ya zama dole a mayar da martani kan zargin da mahukuntan Jami’ar suka fitar domin kan kungiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here