2023: Tinubu ya tuntubi Omole, Jagoran APC a Ingila da tawagar ‘Yan Nigeria a Landan

Tinubu with Omole in London
Tinubu with Omole in London

Bola Tinubu daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC ya karbi bakuncin Mista Ade Omole, shugaban jam’iyyar reshen kasar Birtaniya da tawagar ‘yan Najeriya dake kasar Birtaniya a birnin Landan.

Alhaji AbdulRasaq Danjuma, Mataimakin Omole na musamman ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce Tinubu ya yi taron ne domin tuntubar NDA da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Burtaniya kan kudirin takarar shugaban kasa na 2023 na Tinubu.

Danjuma ya ce sabanin yadda kafafen yada labarai ke yadawa, Tinubu yana cikin koshin lafiya.

A cewarsa, Omóle, ya yi wa Tinubu bayani kan ayyukan ci gaba a Burtaniya da sauran batutuwan da suka shafi ci gaban kasa a gida.

Ya ce Omole ya kuma yi wa Tinubu bayani kan yadda ’yan Najeriya masu kishin kasa a kasashen ketare ke taimakawa daga kasashen da suke zaune domin tabbatar da ingantacciyar Najeriya ga kowa.

Ya kuma kara da cewa, Omole na cewa masu ci gaba a kasar Birtaniya suna hada kai da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa a duniya domin yin aiki kafada da kafada da takwarorinsu na Najeriya domin bunkasa zaman lafiya, hadin kai da ci gaba.

Ya ce ganawar da suka yi da shugaban jam’iyyar APC na kasa ya tabbatar da aniyar al’ummar Nijeriya mazauna kasashen waje wajen gina kasa.

Shi ma Darakta Janar na NDA, Dr Akin Badeji a cikin sanarwar, ya bayyana ayyukan da ake gudanarwa a kasashen waje da ma Najeriya domin tabbatar da ganin an samu nasarar shugabancin Tinubu a 2023, inda ya kara da cewa kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an biya bukatar ta.

Taron ya samu halartar Mista Joseph Adebola, Dr Kenny Ojutalayo, Dr Oladapo Habeeb, Mrs Edith Nwachukwu, Hajia Rakiya Abubakar, Dr Ronke Tomori da Mista Lanre Adegun da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a kasar Birtaniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here