Daukar aikin ‘yan sanda: ‘Yan arewa 104,403 da ‘yan kudu 23,088 ne suka neme aikin

police recruits new
police recruits new

Kimanin mutane 127,491 ne da suka nemi shiga aikin ‘yan sanda, daga ranar Talata za su mamaye hedikwatar ‘yan sandan jihihon da ke fadin kasar domin duba lafiyarsu.

Wadanda suka nema sun hada da mutane 104,403 daga Arewa da 23,088 daga Kudancin kasar nan.

Wani rahoto ya nuna cewa jihar Abia na da masu neman aikin ‘yan sanda 596; Akwa Ibom 3,536; Anambra 314; Bayelsa 759; Cross River 2,704; Delta 976; Ebonyi 463; Edo 1,206; Ekiti 1,417; Enugu 707; Imo 852; Legas 562; Ogun 1,154; Ondo 2,472; Osun 2,006; Oyo 1,767 da Rivers 1,597.

Sauran sune Plateau 4,100; Kebbi 3,596; Katsina 7,605; Kano 7,557; Kaduna 7,436; Jigawa 4,951; Benue 6,578; Adamawa 8,206; Bauchi 7,140; Borno 8,693; Babban Birnin Tarayya 4,418; Kogi 4,412; Kwara 2,410; Nasarawa 4,700; Nijar 4,672; Sokoto 2,450; Taraba 4,075; Yobe 4,992; Gombe, 4,416 da Zamfara 1,990.

Wani Sako da aka aike ya umurci masu nema su jira umarnin ‘yan sanda wanda zai fara aiki daga 1-20 ga Fabrairu.

An umurci masu nema da su bayyana tare da Lambar Shaida ta Ƙasa, kwafi na takaddun shaida, takaddun haihuwa da cikakkun takaddun garanto.

Rundunar ‘yan Sanda ta shawarci jami’an da ke gudanar da aikin tatancewar da su tabbatar sun zabo mutanen da suka cancanta.

An ja hankalinsu da su yi taka tsantsan game da ayyukan cin hanci da rashawa tare da gargadin jami’an da su bi ka’idojin da aka gindaya a cikin dokar ‘yan sanda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here