Me yasa Dimokradiyya ta gaza magance matsalolin Afrika – Obasanjo

Olusegun Obasanjo new 750x430

Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce mulkin demokradiyya ya gaza wajen kawo ci gaba a nahiyar Afrika tare da warware matsalolin da suka dabaibaye ta.

Ya ce tsarin ya gaza ne saboda abin da ya ƙunsa bai zo daidai da al’adu, da yadda ake tafiyar da rayuwa a nahiyar ba, da abubuwan da mutanen nahiyar suka yi amanna da su ba.

Jaridar SoolaceBase ta rawaito cewa, Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abuja, a wurin wani taron bikin cika shekaru 60 a duniya na tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, Emeka Ihedioha.

Tsohon shugaban ya yi nuni da cewa idan aka kalli yadda tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln, ya bayyana tsarin dimokuradiyya da cewa gwamnati ce ta mutane da mutane ke jagoranta domin al’umma.

Karin karatu: Rikicin Natasha da Majalisar Dattijai: Alkali ya janye daga ƙara, tare da ba da dalilai

Inda ya ƙara da cewa tsari ne da ake domin kowa ya amfana, ba wai wani bangare na al’umma ba ko wasu mutane ƙalilan ba.

Obasanjo ya kuma bayyana cewa kafin zuwan dimokuradiyyar ƙasashen yamma, Afrika na da nata tsarin shugabancin wanda ke kula da buƙatun kowa.

A cewarsa wannan tsarin shi ne dimokuradiyya, ba abin da ake kira dimokuradiyya ba a yau wanda ke bai wa shugabanni damar karɓar duk abin da suke so ba bisa ƙa’ida ba da kuma ta hanyar cin hanci da rashawa su ce wa mutane su je kotu idan suna da ja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here