Ministan Sufuri, Sa’id Alkali, ya ce za a gyara sassan titin Abuja zuwa Kaduna da suka lalace cikin kwanaki 10 masu zuwa.
Alkali ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan da ya duba ci gaban da ake ta samu.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an lalata wasu sassan titin jirgin a ranar Talatar da ta gabata bayan wani jirgin kasa da ya taso daga Kaduna ya kauce daga tashar Asham.
A cewarsa, ma’aikatan hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC) sun dukufa ba dare ba rana don ganin an yi aikin sharewa da gyaran layukan da suka lalace da wuri.
Ya yabawa jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a kan kokarin da suke yi na tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji da ma’aikata da kuma cibiyoyin jiragen kasa a wurin.
Ministan, wanda ya ce tawagarsa ta yi adalci kan binciken, amma ya bayyana cewa ba shi da ikon yin riga malam a kan binciken.
Alkali, ya ce za a kwashe taragutsai takwas da abin ya shafa daga wurin nan da kwanaki biyu masu zuwa, ya kara da cewa hanyar titin da hadarin ya rutsa da shi ya kai kimanin mita 150.(NAN)












































