Wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun kai wa ayarin motocin shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Kebbi kuma tsohon ministan shari’a Abubakar Malami hari a ranar Litinin a Birnin Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan dawowar Malami jihar, a lokacin da yake ziyarar jaje ga iyalai da dama a cikin birnin.
Shaidu sun ce kimanin motoci 10 da ke cikin ayarin motocin ne aka lalata, yayin da wasu da dama daga cikin magoya bayansa suka samu raunuka daban-daban.
Malami wanda ya rike mukamin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, ya bayyana harin a matsayin shiri na siyasa.
Karanta: Na yi dacen zabar ka a matsayin mataimakin shugaban kasa – Tinubu ya shaida wa Shettima @59
“Na kasance a Birnin Kebbi ne kawai don jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a lokacin da ba na nan ba, ba don yakin neman zabe ba.

“Abin takaici ne wasu ‘yan daba sun fito daga hedikwatar jam’iyyar APC na jihar, dauke da makamai da duwatsu, suka far wa ayarin mu, inda suka lalata motoci tare da raunata magoya bayanmu.
Sai dai jam’iyyar APC a jihar Kebbi ta musanta cewa tana da hannu a lamarin.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar Isa Assalafy, a wata sanarwa da ya fitar, ya yi tir da harin tare da bayyana Kebbi a matsayin jiha mai zaman lafiya.
“Babu gwamnatin da ke samun gagarumin goyon bayan jama’a kuma tana da yakinin samun nasara a 2027 da za ta so zaman lafiyar jihar ya wargaje,” in ji Assalafy.
Ya kuma yi zargin cewa jami’an tsaro dauke da muggan makamai da ke tare da ayarin Malami ne suka bude wuta a yayin arangamar, wanda ya yi ikirarin ya ta’azzara lamarin.
Har yanzu dai hukumomin ‘yan sanda a Kebbi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
The Punch













































