Na Tabbata Tinubu Zai Kai Najeriya Tudun-Mun-Tsira —Aisha Buhari

Aisha Buhari Katsina
Aisha Buhari Katsina

Matar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta ce tana da yakini cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, zai jagoranci Najeriya zuwa tudun-mun-tsira, saboda hangen nesansa, gogewarsa a siyasa.

Aisha Buhari ta ce da wadannan siffofi da kuma kyakkyawan kudurin da na Tinubu yake da shi ga daukacin al’ummar kasar ba tare da wani bambaci ba, sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasararsa a zaben da aka kammala.

Ta bayyana haka ne a sakon taya murna ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, bisa nasarar da ya samu a zaben da aka kammala.

Aisha Buhari, ta kuma taya zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, murnar cin zabe.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here