Gwamnatin tarayya, PENGASSAN da Dangote sun cimma yarjejeniya kan rikicin matatar mai

PENGASSAN Dangote 860x482 1.jpg 750x430

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta tsoma baki ta kuma sasanta rikicin da ya kunno kai tsakanin ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da kuma kamfanin matatar man fetur ta Dangote.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Dr. Muhammad Maigari-Dingyadi, ya rattaba hannu a kai bayan taron sasanci na kwana biyu da aka gudanar, sannan aka gabatar wa manema labarai a ranar Laraba a Abuja.

Taron, wanda aka gudanar a ranar Litinin da Talata, ya haɗa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ministocin kuɗi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, ministan harkokin man fetur (gas), da kuma jami’an tsaro irin su DSS, NIA, NNPCL, NMDPRA, NUPRC tare da shugabannin ƙwadago.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa wannan sasanci ya biyo bayan umarnin da PENGASSAN ta bai wa mambobinta na dakatar da isar da iskar gas tare da janye ayyuka daga matatar mai ta Dangote.

Karin labari: Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa ta fara kame baƙin da suka wuce wa’adin bizar su a Najeriya

Kungiyar ta yi zargin cewa kamfanin ya sallami ma’aikatansa sama da 800 ba tare da bin ƙa’ida ba, lamarin da ya haddasa yajin aikin.

Sai dai kamfanin Dangote Refinery ya bayyana cewa korar ma’aikatan ta biyo bayan wani sabon tsarin sake fasalin gudanarwa da kamfanin ke aiwatarwa.

A cewar sanarwar, an cimma matsaya cewa yin ƙungiya na ɗaya daga cikin haƙƙin ma’aikata da doka ta Najeriya ta tabbatar, kuma dole kamfani ya mutunta hakan.

Haka kuma, an amince cewa kamfanin Dangote zai fara maido da ma’aikatan da abin ya shafa cikin sauran rassan kamfanonin da ke ƙarƙashinsa ba tare da rage musu albashi ba.

Haka nan, an kuduri aniyar cewa babu wani ma’aikaci da za a ci gaba da tsananta wa saboda shiga wannan rikici.

PENGASSAN ta amince da fara matakan kawo ƙarshen yajin aikin, yayin da ɓangarorin biyu suka yi alƙawarin aiwatar da dukkan yarjejeniyar cikin gaskiya da amana.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here