Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cimma manyan nasarori 12 na tattalin arziki cikin shekaru biyu kacal, ta hanyar aiwatar da manufofin kuɗi da suka haifar da sakamako a zahiri.
Tinubu ya bayyana haka ne a yayin jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya ce sake fasalin da gwamnatinsa ta yi ya fara haifar da gagarumin ci gaba.
A cewarsa, Najeriya ta samu bunkasar tattalin arzikin kasa (GDP) da ya kai kashi 4.23 cikin ɗari a zango na biyu na shekarar 2025, wanda ya dara hasashen kashi 3.4 na asusun ba da lamuni na duniya (IMF).
Haka kuma hauhawar farashin kaya ya ragu zuwa kashi 20.12 cikin ɗari a watan Agustan 2025, mafi ƙanƙanta cikin shekaru uku.
Karin karatu: Gwamnatin tarayya, PENGASSAN da Dangote sun cimma yarjejeniya kan rikicin matatar mai
Shugaban ya ƙara da cewa an wuce burin samun kuɗaɗen shiga daga sashen da ba na mai ba, inda aka tara fiye da Naira tiriliyan 20 tun kafin ƙarshen shekara.
Haka kuma, an samu raguwar matsin lamba daga biyan bashi, daga kaso 97 cikin ɗari zuwa ƙasa da kaso 50.
Tinubu ya ce cire tallafin man fetur ya samar da tiriliyan na naira domin saka hannun jari a masana’antu da kuma shirye-shiryen tallafin talakawa.
Haka nan ya ce ajiyar kuɗaɗen waje ya kai Dala biliyan 42.03, mafi girma tun shekarar 2019.
A ɓangaren haraji, ya bayyana cewa ana faɗaɗa fagen biyan haraji ba tare da ƙara nauyi kan masu biyan haraji na yanzu ba, tare da bayar da sauƙi ga masu ƙaramin ƙarfi.
Tinubu ya kuma bayyana cewa Najeriya ta samu ribar cinikayya tsawon zangon kwata biyar a jere, yayin da fitar danyen mai ya kai ganga miliyan 1.68 a rana, sannan ƙasar ke tace fetur a cikin gida karo na farko cikin shekaru 40.
Ya ce wannan nasara ta haɗu da ci gaban da aka samu a bangaren hakar ma’adinai, musamman Gwal, wanda ya fara bada gudunmawa mai yawa ga GDP.
Dangane da ci gaban ababen more rayuwa, shugaba Tinubu ya ce ana gab da kammala layin dogo na Kano–Katsina–Maradi da Kaduna–Kano, haka kuma aikin babbar hanyar Legas–Calabar da Sokoto–Badagry na ci gaba.
Karanta: Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa ta fara kame baƙin da suka wuce wa’adin bizar su a Najeriya
Ya ƙara da cewa hukumar zartaswar tarayya ta amince da Dala biliyan 3 domin kammala aikin layin dogo na gabashin kasar nan.
Ya bayyana cewa kasuwar hannun jarin Najeriya ta samu gagarumar nasara, inda ta tashi daga maki 55,000 a watan Mayu 2023 zuwa sama da maki 142,000 a watan Satumba 2025.
A cewarsa, babban bankin Najeriya (CBN) ya rage riba a karo na farko cikin shekaru biyar, alamar kwanciyar hankali a tattalin arziki.
A karshe, ya jaddada cewa gwamnatin tarayya tana ci gaba da mayar da hankali kan tsaro da kawar da ta’addanci domin samar da yanayi mai kyau da zai taimaka wa tattalin arziki ya bunƙasa.
NAN













































