Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa ta fara kame baƙin da suka wuce wa’adin bizar su a Najeriya

visa naija 750x430

Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS) ta ce ta fara wani aiki na musamman a duk fadin ƙasar domin kame bakin da suka wuce wa’adin bizar su ko suka karya sharuddan shigowa Najeriya.

A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Akinsola Akinlabi, ya fitar a ranar Laraba a Abuja, ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan karewar wa’adin tsarin sassauci na gwamnatin tarayya da ake kira Expired Visa Initiative (Amnesty), wanda ya ƙare da tsakar daren 30 ga Satumba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa shirin sassauci da aka sanar tun ranar 5 ga Yuli ya bai wa bakin da bizar su ta ƙare damar gyara matsayinsu na masu shige da fice a Najeriya ba tare da biyan tara ko fuskantar hukunci ba.

Akinlabi ya ce aikin kamun zai fara ne daga 1 ga Oktoba, inda zai shafi masu biza iri daban-daban da wa’adin ta ya ƙare.

Ya lissafa su da masu Visa on Arrival (VoA) da ta ƙare, masu biza ta shigar lokaci ɗaya ko ta yan kasuwa (short visit ko business visa), da kuma masu izinin zama da aiki na musamman da aka sani da CERPAC da ta ƙare.

Ya bayyana cewa duk wani baƙon da aka samu da laifin karya dokokin shige da ficen Najeriya zai fuskanci hukunci mai tsauri, wanda zai haɗa da biyan tara, fitar da shi daga ƙasar, da kuma hana shi sake shigowa Najeriya a nan gaba.

Dangane da tarar da za a yi, ya ce, ƙasa da watanni uku da wuce wa’adin biza zai jawo fitarwa daga ƙasar, da tarar ta dalar Amurka 15 a kowace rana, ko kuma a zaɓi hana shigowa Najeriya har tsawon shekaru biyu.

Idan ya haura watanni uku amma bai kai shekara ba, tarar ta kai dalar Amurka 15 a kowace rana, tare da yiwuwar hana shigowa har tsawon shekaru biyar.

Idan kuma ya kai shekara guda ko ya wuce, hukuncin ya haɗa da fitarwa da kuma hana shigowa har abada ko aƙalla shekaru goma.

Akinlabi ya jaddada cewa hukumar kula da shige da fice ta Najeriya za ta ci gaba da bin doka da oda wajen tafiyar da al’amuran shige da fice, kare tsaron ƙasa da kuma tabbatar da gaskiya da inganci a dukkan matakan gudanarwa.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here