Jerin Sunaye: Tinubu ya ba ‘yan gwagwarmayar 12 ga Yuni lambobin yabo ta kasa

Bola Tinubu scaled 1 750x430 1

Shugaba Bola Tinubu a ranar Juma’a ya sanar da sake farfado da Cibiyar Nazarin Man Fetur da ke Kaduna da kuma sauya sunan ta zuwa suna marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua.

Tinubu ne ya sanar da haka a jawabin sa na ranar Dimokuradiyya ga al’ummar kasa.

Shugaban ya kuma amince da baiwa ‘yan gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya da jami’an soji da dama da suka taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar 12 ga Yuni lambobin yabo ta kasa.

Ya bayyana Yar’Adua a matsayin daya daga cikin masu tsara dimokuradiyyar Najeriya ta wannan zamani, wanda hangen nesa sa ya taimaka wajen tsara yadda dimokuradiyyar kasar ta samo asali.

“Daga cikin masu tsara dimokuradiyyar Najeriya ta zamanin nan, muna karrama Janar Shehu Musa Yar’Adua saboda hangen nesa sa na hadin kan kasa.

“Don karrama gudummawarsa, Gwamnatin Tarayya ta amince da sake farfado da Cibiyar Nazarin Man Fetur da ke Kaduna da ta sabunta da kuma sauya sunan ta zuwa Jami’ar Kimiyyar Geoloji da Fasahar Injiniya ta Janar Shehu Musa Yar’Adua,” in ji shi.

Tinubu ya kuma sanar da baiwa wasu ‘yan Najeriya da dama lambobin yabo ta kasa wadanda, ya ce sun sha azaba, gudun hijira, dauri da sauran wahalhalun gwagwarmayar dimokuradiyya.

Wadanda aka zaba domin karraman sun hada da Ayoka Lawani, Tunde Fagbenle, Oladele Alake, Olatunji Bello, Louis Odion, Segun Babatope, Sam Omatseye, Ademola Osinubi, Bolawole, Lade Bonuola, Femi Kusa, Debo Adeniran da Ayo Opadokun.

Sauran sun hada da Ralph Obiora, Ose Osayande, Osa Director, Sylvester Odion-Akhaine, Arthur Nwankwo, Osagie Obayuwana, Joe Okei-Odumakin, Titus Mann, Joe Igbokwe, Richard Akinnola da Ben Charles-Obi.

George Mbah, Niran Malaolu, Janar Ishola Williams (mai ritaya), Femi Aborisade, Jenkins Alumona, Gbemiga Ogunleye, Muyiwa Adekeye, Babajide Kolade-Otitoju da Ike Okonta suma an karrama su.

Shugaban ya kuma karrama jami’an soji da ya kira “sojojin-dimokuradiyya” wadanda suka goyi bayan gwagwarmayar 12 ga Yuni.

Sun hada da Manjo Janar M.A. Garba, Birgediya Janar Jaafaru Isa, Kanar Farouk Ahmed, Kanar Sambo Dasuki, Kanar Lawan Gwadabe, Birgediya Janar Jonathan Temlong, Kanar Musa Shehu, Manjo Janar Chris Eze da Manjo Janar Harris Dzarma.

Sauran sun hada da Kanar Isa Jibrin, Manjo Janar Joseph Oshanupin, Kanar Olusegun Oloruntoba, Laftanar Kanar Kefas Bulus, Kanar J. Okai, Kanar Emmanuel Ndubueze, Laftanar Kanar Yakubu Muazu da Birgediya Janar Yahaya Abubakar, wanda yanzu shi ne Etsu na Nupe.

Tinubu ya ce cikakken jerin wadanda za a ba su lamba za a fitar da shi cikin kwanaki masu zuwa.

Yayin da yake nazari kan tafiyar dimokuradiyyar Najeriya, shugaban ya ce bambancin kasar, wanda da a baya ana ganin sa a matsayin matsala, yanzu ya zama daya daga cikin ginshikan da ke rike da dimokuradiyya a kasar.

“Shekaru 27 da suka gabata, mutane da yawa sun yi shakkar dDimokuradiyyaimokuradiyya za ta tsira a nan saboda bambancin mu. A yau, bambancin mu ne ke rike da dimokuradiyyar mu.

“Tafiyar da ke gabanmu tana da tsauri, amma 12 ga Yuni ya tunatar da mu ‘yan Najeriya ba su karye ba. Muna lankwasuwa, muna zub da jini, amma ba mu karye ba,” in ji shi.

Ya roki ‘yan Najeriya su sabunta kudurin su na rike da ka’idojin dimokuradiyya da gina kasa.

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya albarkaci jaruman dimokuradiyya da Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, yayin da yake taya ‘yan kasa murnar bikin Ranar . (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here