Tuggar ya yi rashin nasara a zaben fidda gwanin gwamna na APC a Bauchi

Ambassador Yusuf Tuggar

Tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yi rashin nasara a kokarinsa na samun tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027 mai zuwa a Jihar Bauchi.

Bayan jinkirin da ya na sa’o’i, AIG John Abang (mai ritaya), Shugaban Kwamitin Zaben Fidda Gwani na Gwamna da Majalisar Dokoki na APC a Jihar Bauchi, ne ya sanar da sakamakon a safiyar ranar Asabar.

A cewar Abang, tsohon Gwamna Mohammed Abubakar ne ya samu nasara, bayan doke sauran ‘yan takara shida a zaben.

Ya sanar da sakamakon kamar haka: Abubakar ya samu kuri’u 57,517, wanda ya yi nasara, sai kuma Tugger da ya samu kuri’u 26,001, yayin da Nura Manu Soro ya samu kuri’u 13,638.

Sauran ‘yan takarar da suka fafata sun hada da Bala Maijama’a A. Wunti, wanda ya samu kuri’u 13,648, da Kabir Baba Ma’aji da kuri’u 8,157, Baba Abubakar Suleiman, wanda ya samu kuri’u 7,688, da Yakubu Yakubu Abdullahi, wanda ya samu kuri’u 7,181.

Ana tunawa cewa Gwamna mai ci na Bauchi, Bala Mohammed, ya doke ɗan takar gwamna na APC na 2027 a shekarar 2019.

Mohammed ya fafata kuma ya yi nasara a zaben karkashin jam’iyyar PDP, yayin da Abubakar ya yi rashin nasara a matsayin gwamna mai ci karkashin jam’iyyar APC.

Tuggar yana cikin mutane na farko wadanda aka nada da suka yi biyayya ga umarnin Shugaba Bola Tinubu suka ajiye aikinsu don yin takara a zaben 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here