Gwamnatin Kano ta sanar da ranar fara hutun zangon karatu na biyu a Makarantu

Abba Yusuf Kano Governor1

Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairun 2025 a matsayin ranar hutu na zango na biyu ga dukkan makarantun kwana da na firamare masu zaman kansu da na gaba da firamare a jihar.

Wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar ta bayyana cewa daliban makarantun kwana za su koma makarantunsu a ranar Lahadi 6 ga Afrilu 2025 yayin da daliban za su koma ranar Litinin 7 ga Afrilu 2025.

Don haka, sanarwar ta bukaci Iyaye/Masu kula da Dalibai a makarantun kwana da su je daukar yaransu da sanyin safiyar Juma’a 28 ga Jumu’a 2025.

Sai dai sanarwar ta ruwaito kwamishinan ma’aikatar Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda ya bukaci iyaye/Masu kula da dalibai da daliban makarantun da su tabbatar da bin ka’idoji wajen komawa makarantunsu ranar da aka sanar.

Ya yi gargadin cewa za a dau matakin ladabtarwa a kan Daliban da suka karya doka.

Kwamishina Makoda ya yaba da hadin kai da goyon bayan da ake baiwa ma’aikatar tare da yi wa Dalibai da iyayensu fatan ganin watan Azumin Ramadan lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here