Ba za mu sake tsawaita lokacin yin rajistar UTME bayan cikar wa’adi – JAMB

JAMB Prof. Ishaq Oloyede 750x430

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta ce ba za ta sake tsawaita lokacin yin rajistar jarrabawar shiga manyan makarantu ta 2025 (UTME) ba bayan ranar 8 ga watan Maris.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Dr Fabian Benjamin ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Talata.

Benjamin ya ce wa’adin rajistar da ya fara a ranar 3 ga Fabrairu, zai kare ne a ranar 8 ga Maris, 2025.

A cewarsa, an sanar da wannan wa’adin a fili a duk tallace-tallace da kalandar hukuma don fara aikin UTME na 2025.

Ya kara da cewa a halin yanzu, sama da dalibai miliyan 1.5 ne suka yi nasarar yin rajista, wadanda suka yi daidai da hasashen hukumar a 2025.

Benjamin ya karfafa wa dalibai gwiwa da su kammala rajista da wuri tare da bin ka’idojin da aka kayyade na jarrabawar UTME 2025. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here