Kaduna ta kaddamar da shuwagabannin gudanarwa na manyan makarantu gaba da sakandare 3

B9A4833A BBFF 4AD1 9979 B391CC6D664F
B9A4833A BBFF 4AD1 9979 B391CC6D664F

Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da majalisar gudanarwar manyan makarantun gaba da sakandare guda uku.

Makarantun sun hada da: Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Nuhu Bamali Polytechnic, Zariya, da Kwalejin Ilimi, Gidan Waya.

Da take kaddamar da shugabannin a Kaduna, kwamishiniyar ilimi Halima Lawal, ta ce an zabo ‘yan majalisar ne bisa la’akari da kwarewarsu.

“An zaɓe ku ne bisa tsarin sadaukarwa, kishin ƙasa da gogewa. Ana sa ran za ku yi amfani da  kwarewarku wajen gudanar da ayyukanku don ci gaban fannin ilimi gaba daya. Kuna da babban aiki a gabanku kuma muna da tabbacin za ku yi nasarar aiwatar da ayyukanku cikin nasara,” inji ta.

An kaddamar da Mista Hussaini Dikko a matsayin Shugaban Hukumar Gudanarwar KASU tare da magatakardar Jami’ar, Mista Samuel Manshop a matsayin sakatare da Mista Ismail Afieza mai wakiltar kamfanoni masu zaman kansu.

Sauran membobin sun hada da: Dr Tanimu Meyere, Habiba Sani, Charity Shekari, Mataimakiyar shugabar gwamnati, Farfesa Muhammad Tanko, mataimakan shugabannin jami’o’i biyu, da babban sakataren hukumar kula da jami’o’i ta kasa.

Sauran sun hada da wakilan majalisar dattawan KASU guda biyu, sai kuma sakatarorin dindindin na ma’aikatun lafiya da kudi.

Haka kuma an kaddamar da Dr Ishaya Dare-Akau a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na Nuhu Bamali Polytechnic tare da Mista Haruna Uwais mai wakiltar kungiyar masana’antun Najeriya, Mrs Gladys Goje da Dr Salisu Kubau.

Sauran mambobin sun hada da shugaban majalisar dattawa, da sakatarorin dindindin na ma’aikatun lafiya da kudi, mamba a hukumar ilimi, da wakilan kungiyar injiniyoyi ta Najeriya, jami’ar Ahmadu Bello da ma’aikatar shari’a.

Farfesa Binta Abdulrahman ita ce shugabar Majalisar gudanarwa ta Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya, tare da Kabiru Ajuji, Mista Masa’udu Igabi, Mista Bayie Dauda a matsayin membobin da ke wakiltar al’umma.

Sauran mambobin sun hada da Provost na Kwalejin, Farfesa Alexander Kure, da Sakatarorin dindindin na Ma’aikatun Kudi, Ilimi, da Shari’a. Sauran su ne: wakilai biyu na Hukumar Ilimi, ma’aikatan da ba na ilimi ba, da Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Kasa.

A nasu tsokaci na daban, shugabannin makarantun, Dikko, Dare-Akau da Abdulrahman, sun godewa gwamnatin jihar Kaduna da ta same su a matsayin wadanda suka cancanci wannan nauyi.

Sun yi alkawarin bayar da gudunmowarsu tare da mayar da makaratun zuwa nagartattu domin ci gaban fannin ilimi baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here