Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar shirya jarabawar yammacin Afirka (WAEC) da kuma hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO su koma yin amfani da na’ura mai kwakwalwa (CBT) don gudanar jarrabawar daga watan Mayu/Yuni 2026.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake sa ido kan jarabawar da jami’an hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB ke gudanarwa a Bwari, Abuja, ranar Litinin.
Dakta Tunji Alausa ya bayyana cewa WAEC da NECO za su fara gudanar da aikinsu ta hanyar amfani da CBT daga watan Nuwamba, kuma za a fara ne a lokacin jarrabawar Mayu/Yuni 2026.
“Idan JAMB ta samu nasarar gudanar da jarabawar CBT ga ‘yan dalibai sama da miliyan 2.2, WAEC da NECO ma za su iya yin haka.
Alausa ya jaddada kudirin gwamnati na sauya tsarin rubutu jarrabawar ta CBT gaba daya, yana mai cewa a jarrabawar WAEC na Mayu/Yuni 2026 za ta zama cikakkiyar jarrabawa ta Kwamfuta.
Karin karatu: 2025: JAMB ta fara UTME na masu bukata ta musamman, ta bayyana nasarorin da cibiyar Kano ta samu
Ministan ya kuma bayyana cewa an kafa wani kwamiti da zai duba ma’aunin jarrabawa a fadin kasar.
Ya yi nuni da cewa, ana sa ran gabatar da shawarwarin kwamitin nazari a wata mai zuwa, wanda ke nuni da cewa an kara yin garambawul a fannin ilimi.