Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta kalubalanci gwamnatin tarayya da ta karba tsarin biyan albashi na University Transparency and Accountability, UTAS, domin ta janye yajin aikin da ta tsunduma. Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya sanar da hakan yayin zantawa da gidan talabijin na Channels a daren Litinin, yace zasu cigaba da yajin aikin har sai gwamnati ta karba UTAS kuma ta karrama yarjejeniyar su ta 2009
Idan za a tuna, ASUU ta shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 wanda a ranar Litinin din nan ne ta cika kwanaki 140.