JAMB ta amince da yin rijista kyauta ga masu bukata ta musamman

JAMB
JAMB

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta ce masu bukata ta musamman da ke son zana jarrabawar ta 2024/2025 za su iya yin rajista kyauta.

Magatakardar hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da rajistar masu sha’awar shiga jami’a a fadin kasar nan.

Karanta wannanJAMB zata fara Jarrabawar auna fahimta ga masu neman shiga Jamia’a kai tsaye

A yayin da yake sanar da cewa za a fara rajistar jarrabawar share fagen shiga jami’a ta 2024 a ranar Litinin, (wato yau), Oloyede ya ce JAMB za ta ba da takardun yin rijista kyauta ga dukkan nau’ukan masu bukata ta musamman a matsayin tallafi.

Oloyede wanda ya bayyana cewa an samar da matakan da za a tabbatar da gudanar da aikin ga dukkan Dalibai, ya ce a yanzu za a samar da littattafan sauti ga masu lalurar gani.

Karanta wannan: Gwamna Abba ya nada Ganduje a matsayin mamba na majalisar dattawan Kano 

Magatakardar ya ce, wannan ci gaban zai zo ne cikin nau’o’in sauti kamar MP3 da WMV, da kuma WMA wanda zai dace da duk na’urorin da za su iya daukar bayanan sauti.

Ya ce an ba da shawarar samar da littattafan kaset ne a babban taron kasa na farko kan daidaita damarmakin samun ilimi mai zurfi a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here