Malamai hudu na Jami’ar Tarayya Dutse sun shiga cikin kashi 2% na manyan masana kimiyya a duniya

WhatsApp Image 2025 10 06 at 21.38.19 750x430

Jami’ar Tarayya Dutse (FUD) da ke Jihar Jigawa ta samu babban ci gaba a fannin binciken kimiyya, bayan masana kimiyya hudu daga jami’ar sun shiga cikin jerin kashi 2 cikin 100 na manyan masana kimiyya a duniya na shekarar 2025.

Wannan na zuwa ne bisa sabon jerin sunayen da cibiyar sadar da Masana Kimiyya ta Duniya (Top Scientists Network – TopSciNet) ta fitar.

A cewar sanarwar da Daraktan Harkokin Jama’a na FUD, Malam Abdullahi Bello, ya fitar a ranar Litinin, wannan bincike na shekara-shekara na duba masana kimiyya bisa tasirin bincikensu, yawan ambaton ayyukansu da kuma yawan gudunmawarsu a fannin kimiyya, inda yake ware su cikin kashi 2 cikin 100 na kwararru a fannoni daban-daban.

An bayyana cewa Jami’ar Stanford ta Amurka ce ke shirya wannan jerin sunaye ta hannun Farfesa John P. A. Leonidis tare da tawagarsa.

Sanarwar ta ce hakan na nuni da irin tasirin da masana FUD ke samu a fagen bincike na kasa da kasa.

Masana kimiyya da aka yaba da su daga FUD da matsayinsu a jerin na duniya sun hada da:

Dr Sulaiman Tukur Abdulkadir – Matsayi na 39,579

Dr Yusuf Abdullahi – Matsayi na 55,154

Dr Jibrin Muhammad – Matsayi na 312,407

Dr Hafeez Yusuf Hafeez – Matsayi na 388,319

Shugaban jami’ar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, ya jinjinawa masana kimiyyar bisa wannan nasara da suka samu, yana mai cewa hakan hujja ce ta jajircewar jami’ar wajen bunkasa bincike da kirkire-kirkire.

Ya kara da cewa wannan yabo yana kara girmama FUD a idon duniya, tare da zama abin koyi ga matasa da ke tasowa a fannin binciken kimiyya a Najeriya.

Haka kuma, ya bayyana cewa wannan nasara ta kara tabbatar da matsayin jami’ar a matsayin cibiyar bincike mai tasiri a yankin Yammacin Afirka, da kuma jajircewarta wajen gudanar da binciken da ke magance matsalolin kasa da duniya baki daya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here