Gwamnatin jihar Kaduna tace za ta kori malaman makaranta 233 da aka samu da yin amfani da takardun bogi.
Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar KADSUBEB Tijjani Abdullahi, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a yau Alhamis.
Abdullahi ya ce a cikin watan Afrilun da ya gabata ne hukumar ta fara gudanar da wani shirin tantance takardun karatun malaman don tabbatar da cewa malaman makarantu a jihar sun cancanta.
Ya ce a yayin aikin, an tattance malamai 451 kuma daga ciki an samu malamai 233 suna amfani da takardun bogi, wanda ya kai kashi 51% na malaman da aka tantance.
Shugaban na KADSUBEB, ya ce hukumar za ta kori malaman da aka samu da laifin su 233, kuma za a tura sunayensu ga Ma’aikatar Shari’a ta jiha don ɗaukar matakin shari’a a kan su.
Ya kara da cewa za a wallafa sunayensu a shafin intanet na gwamnatin jihar Kaduna.













































