Tsohon shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu Joseph Wayas ya rasu a wani asibiti a Landan.
Ya mutu ne bayan doguwar jinya yana da shekara 80.
An haifi Wayas ne a garin Basang da ke Obudu a Jihar Kuros Riba a ranar 21 ga Mayu, 1941.
Ya yi karatun sakandare a Dennis Memorial Grammar School, Onitsha kafin ya tafi kasar Ingila inda ya yi karatu a Higher Tottenham Technical College, London.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya kuma halarci Kwalejin Kasuwanci, Kimiyya da Fasaha ta West Bromwich, Birmingham da Jami’ar Aston, Birmingham.
Ways ya zama shugaban majalisar dattawa na uku a shekarar 1979 zuwa 1983 kafin juyin mulkin da aka nada Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa na Najeriya.
Wayas ya kasance memba ne kuma wanda ya kafa jam’iyyar APP da aka soke a yanzu.
Daga baya ya shiga jam’iyyar adawa ta PDP a shekarar 2002.
Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade ya sanar da rasuwar shugaban majalisar dattawan a jamhuriya ta biyu, Dr Joseph Wayas.
Gwamna Ben Ayade ya bayyana mutuwar Wayas a matsayin “babban rashi ga jihar Cross River musamman da ma Najeriya baki daya”.
Ya jajanta wa iyalan Dr Wayas, yana mai tabbatar musu da cewa rasuwarsa rashi ce ga kowa, inda ya kara da cewa, “muna tare da ku a wannan lokacin na bakin ciki. Kuna cikin zukatanmu da addu’o’inmu.”













































