Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu da ake zargin ‘yan daba ne da suka kona ofishin Sanata Barau Jibrin, sanata mai wakiltar Kano ta Arewa da ke kan hanyar Maiduguri a cikin birnin jihar.
Solacebase ta ruwaito cewa wasu daruruwa da ake zargin ‘yan daba ne a ranar Alhamis sun lalata ofishin yakin neman zaben Sanata Barau Jibrin tare da kona wasu abubuwa daga bisani kuma suka far wa wasu mazauna yankin.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta tabbatar da kama wadanda ake zargin, a ranar Alhamis yayin da aka gabatar da su.
Yace an kama ‘yan daba 13 dauke da manyan makamai da kayan mayr.
Yace “A yau 02/12/2021 da misalin karfe 0800 na safe ne aka samu rahoto cewa wasu ‘yan daba dauke da muggan makamai sun far wa ofishin Sanata Barau Jibrin, Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa da ke kan titin Maiduguri.”
Bayan samun rahoton ne, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, ya bada umarni ga rundunar ‘Operation Puff Adder’ da su garzaya wurin da lamarin ya faru, domin tabbatar da doka da oda.
Sanarwar ta kara da cewa “an kama mutane goma sha uku da ake zargin ’yan daban ne, kuma an kwato musu abubuwa da suka hada da muggan Makamai guda 34 da Gora 23 dakuma Galan 2 da ake zargin na man fetur ne sai Fakiti 1 dauke da wani ganye da ake zaton wiwi ne.
Sauran abubuwan sun hada da fakiti 24 na maganin Diazapam dakuma Wayar Hannu guda daya, dakuma wasu layu.
Sanarwar tace tuni zaman lafiya ya dawo a yankin inda aka fara bincike a kai kuma za a gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban kotu.













































