Kaduna: Ana sake gudanar da jarabawar Kwarewa ga malamai

2d4ef9e1 el rufai
2d4ef9e1 el rufai

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara gudanar da jarabawar kwarewa ga malaman firamare domin tabbatar da an samar da tsarin koyo da koyarwa mai inganci a jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai a yayin fara jarabawar wadda ake yi ta na’ura mai kwakwalwa wato Computer a yau talata, Shugaban hukumar Ilimin bai daya ta jihar Kaduna Tijjani Abdullahi, ya bayyana cewa ba wai don a kori malamai aka shirya jarabawar ba, an shirya ta ne domin gano inda ake da matsala daga bangaren malamai ta yadda za’a shirya musu horo na musamman domin su kara samun kwarewa.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa malaman zasu amsa tambayoyi guda goma akan ko wane darasi, wanda suka hada da Harshen Turanci da Lissafi da kuma Ilimin Kimiyya.

Idan za’a iya tunawa, kusan shekaru hudu da suka gabata gwamnatin jihar ta taba gudanar da makamanciyar wannan jarabawa, wanda haka ya janyo korar malamai dubu ashirin da biyu da suka fadi jarabawar daga aiki.

Hakan ya sanya kungiyar malamai ta kasa da kungiyar kwadago reshen jihar Kaduna suka gudanar da zanga-zangar lumana domin domin kin amincewa da korar malaman daga aiki. Duk kuwa kurar da aka tayar kan wannan batu gwamnatin Kaduna ta aiwatar da kudirin korar malaman, inda daga bisani ta dauki sabbin malamai kimanin dubu ashirin da biyar domin maye gurbin wadanda aka kora.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here