Buhari zai je Legas don halartar taron kaddamar da littafi

WhatsApp Image 2021 12 08 at 1.23.59 PM
WhatsApp Image 2021 12 08 at 1.23.59 PM

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai je jihar Legas a ranar alhamis mai zuwa domin halartar taron kaddamar da littafin tarihin Bisi Akande tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC.  Mai taken ‘My Participations’.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Tunde Rahman mataimaki na musamman ga tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu kan yada labarai ya fitar. Inda ya bayyana cewa za’a gudanar da taron a Eko Hotels and Suites dake Victoria Island a jihar Lagos.

Sanawar ta ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari shine zai kasance babban bako na musamman, yayin da jagoran APC na kasa Bola Tinubu zai kasance babban bako, inda gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu zai kasance mai masaukin baki..

A tsokacin da yayi a cikin littafin, shahararren marubucin nan Wole Soyinka ya bayyana Bisi Akande a matsayin wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban kasar nan.

Bisi Akande kwararren Akanta ne wanda ya fara aiki a wani kamfani da yake aikin da ya shafi man fetur da gas.

Ya fara siyasa tun daga matakin farko inda ya taba kasancewa Kansila a mazabar Ila-Orangun, dake jihar Osun, kafin daga bisani a zabe shi a matsayin dan majalisar jihar a shekarar 1977.

A shekarar 1979 Gwamnan jihar Oyo a wancan lokaci Bola Ige, ya nada Akande a matsayin sakataren gwamnatin jihar, yayin da a shekarar 1983 ya kasance mataimakin gwamnan jihar ta Oyo.

Haka kuma ya kasance daya daga cikin ‘yan siyasar da da gwamnatin soji ta daure a kurkuku bayan an yi juyin mulki na jamhuriya ta biyu a shekarar 1983. Bayan ya fito daga kurkuku a shekarar 1985 ya sanar da cewa ba zai kara shiga harkokin siyasa ba.

Amma daga baya ya fada cikin wata gwagwarmaya inda ya yi ta suka ga gwamnatin soji, wanda hakan ta kai shi ga zama shugaban kungiyar Yarbawa ta Afenifere a jihar Osun

A shekarar 1999 an zabi Bisa Akande a matsayin gwamnan jihar Osun a karkashin Jam’iyyar AD.

 

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here