Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa (JAMB) ta saki sakamakon jarrabawar UTME na shekarar 2026 na daliban da shekarunsu ba su kai yadda doka ta tanadar ba.
Wannan bayanin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mai ba hukumar shawara kan harkokin sadarwa, Fabian Benjamin, ya fitar ranar Asabar a Abuja.
Sai dai, Benjamin ya bayyana cewa sakin sakamakon jarrabawar ba yana nufin cewa dukkan daliban da ba su kai shekarun ba sun cancanci shiga jami’a, domin kuwa sai wadanda suka cika sharudda na musamman ne kadai za a dauka.
Ya ce dalibin da bai kai shekarun da ake bukata ba na jarrabawar shekarar 2026, shi ne duk wanda shekarunsa ba su kai 16 ba kafin ranar 30 ga Satumba, 2026.
Ya kara da cewa an saki sakamakon ne da farko domin bai wa dalibai da iyayensu damar sanin kokarinsu a jarrabawar.
A cewarsa, ba za a iya amfani da irin wannan sakamakon ba wajen neman gurbin karatu ko wani aiki na hukuma ba, sai dai idan ya shafi daliban da suka cika sharuddan da aka tsara na dalibai da ba su kai shekaru ba amma sun nuna kwazo na ban-mamaki.
Ya ce dalibai za su iya duba sakamakon jarrabawarsu ta hanyar tura kalmar “RESULT” zuwa lambobi 55019 ko 66019 ta amfani da lambar wayar da suka yi rajistar jarrabawar UTME da ita.
Benjamin ya ce hukumar ta riga ta tsara cewa sai daliban da suka nuna hazaka ta musamman kuma suka cika sharuddan da aka tsara ne kadai za a duba yuwuwar ba su gurbin karatu.
Sakamakon haka, ya shawarci daliban da ba su cika sharuddan ba da kada su kai sakamakonsu ga kowace makaranta ko wani mutum da nufin neman gurbin karatu.
Ya bayyana cewa tsarin daukar daliban na musamman yana da matukar tsauri kuma ya kunshi matakai da dama na tantancewa domin tabbatar da cewa sai daliban da suka nuna hazaka ta musamman ta ilimi da fasaha ne kadai za a baiwa.
Ya ce daya daga cikin sharuddan shi ne samun mafi karancin maki 320 a jarrabawar UTME, tare da samun akalla kashi 80 cikin dari na sakamako mai kyau a darussan jarrabawar sakandare (SSCE) da suka dace, inda hakan ya shafa.
“Irin wadannan daliban ana bukatar kuma su cika sharuddan jarrabawar Post-UTME na jami’o’in da suka zaba, sannan ayi musu tantancewa ta karshe da masana za su yi,” in ji shi.













































