Gwamnati tarayya ta amunci da sakin kudi naira miliyan 964 don samar da kayan karatu na zamani a makarantu uku na kowace jiha a fadin Najeriya.
Ministan yada labarai, Lai Mohammed, ne ya sanar da hakan bayan kamala taron maso zartawa, wanda shugabankasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba a fadarsa da ke Abuja.
Ministan yada labarain ya ce, gwamnatin zata kashe kudi kimanin miliyan 964 don samar da kayan karatu na zamani a piramare dai dai a shiyoyi uku da muke dasu a kowace jiha ta Najeriya.
Wadanda zasu amfana da kayan aikin a shiyoyin sun kai 4,360, sanan kuma gwamnatin zata raba wayoyi kirar android guda 4,360 da kuma samar da wuta mai amfani da hasken rana a kowace makaranta data rabauta da aikin.