jam’iyyar PDP ta maida martani kan batun ciyo bashin da Ganduje zai yi

Peoples Democratic Party
Peoples Democratic Party

Jam’iyyar PDP Ba ta ce bata Goyon Bayan Ciyo Bashin 10 Billion Naira da Gwamnatin Kano Zatayi Don Sanya Na’urar  Zamani ta CCTV Dazummar Magance Matsalar Tsaro.

Jam’iyyar PDP Ta Bakin Sakataren Yada Labaran ta na Kano HON BASHIR SANATA ta ce so ake a fake da (Guzuma a harbi Karsana) Ma’ana afitar da Kudin da Sunan Tsaro a karkatar dasu zuwa ga wani abun na Daban.

Kuma Ba komai ne Matsalar Tsaro ba illa Rashin ilimi ga matasa dakuma Rashin aikin yi,

Idan Har aka samarwa matasa aikin yi aka samar musu ingattaccen ilimi to Hakika anyi maganin Kaso 85 % na Matsalar Tsaro.

A wannan lokacin da Jam’iyyar APC Mai mulki ta lalata tattalin arziki, Suka haifar da Rashin Ruwan Sha da na ibada, APC ta je fa mutanen kasa acikin fatara, talauci, Wanda abinci ma wahala yake wa talaka Ina ga Kuma biyan kudi Jarabawa Kimanin #23000 Wanda ‘Daliban ba su da Kudin iyayen su ma basu ajiye ba Sanadiyyar hakan wasu yaran karatun su zai lalace su koma Shaye – Shaye daga nan Rayuwar su ta Gur6ata Sai Kuma abin da hali yayi.

Allah yakawo mana Gwamnati Mai Kishin ilimi da Kuma kishin Talakawa.

Daga  Bashir Sanata

P.R.O  PDP KANO STATE

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here